Mutane 34 sun mutu a mummunan hatsarin jirgin kasa a Kongo

Akalla mutane 34 ne suka mutu inda wasu 40 suka jikkata sakamakon hatsarin jirgin kasa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Mutane 34 sun mutu a mummunan hatsarin jirgin kasa a Kongo

Akalla mutane 34 ne suka mutu inda wasu 40 suka jikkata sakamakon hatsarin jirgin kasa a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Jirgin kasan mallakar kasar Kongo ya yi karo da gini tare da kama wuta a tashar jiragen kasa da ke kudancin lardin Lualaba.

Sajan Simon Tongwa ya shaida wa 'yan jaridu cewa, jirginn kasan na dauke da fasinjoji, kayan abinci da man fetur kuma hatsarin ya afku ne a lokacin da ya sauka daga kan layin dogo.

Ya ce, 'yan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin.Labarai masu alaka