'Yan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 3

Akalla sojojin Najeriya 3 ne suka mutu yayinda wasu 6 suka samu raunuka sakamakon fafata rikici da 'yan ta'addar Boko Haram a yankin arewa maso-gabashin kasar.

Laftanal Kanal Samuel Kingsley na runduna ta 7 ya shaida cewa, lamarin ya afku ne a lokacin da dakaun gwamnatin Najeriya ke ci gaba da fatattakar 'Yan Boko Haram a maboyarsu da ke dajin Sambisa.

Dajin Sambisa dai shi ne mafakar Boko Haram ta karshe da ke jihar Borno.

An kwashe jikkunan wadanda suka mutu yayinda ake ci gaba da kula da wadanda suka samu raunuka. 

A yayin farmakan da sojojin najeriya suka kai sun fatattaki 'yan ta'addar Boko Haram daga kauyukan Talala, Ajigin, Mangzum, Abagajiri, Kafa, Dusula, Buk, Malumti, Abulam, Shyadawe-Angwan-Fulani, Shyadawe-Angwan-Bula-Musa, Shyadawe da sauransu.

Dakarun sun kuma kwace makamai, babura, akori-kura, kwamfuta injinan tara mai daga hannun 'yan ta'addar.Labarai masu alaka