Wata cuta da ba a san irin ta ba na kashe mutane a Gana

Dalibai 4 sun rasa rayukansu sakamakon bullar wata sabuwar cuta da ba a taba ganin irin ta ba a kasar Gana da ke Yammacin Afirka.

Wata cuta da ba a san irin ta ba na kashe mutane a Gana

Dalibai 4 sun rasa rayukansu sakamakon bullar wata sabuwar cuta da ba a taba ganin irin ta ba a kasar Gana da ke Yammacin Afirka.

Ministan Yankin Ashanti Simon Osei Mensah ya bayyana cewa, a ranar Talatar nan wasu daliban makarantar sakandire ta Kumasi 4 sun mutu sakamakon kamu wa da wata cuta da ba a san irin ta ba.

Mensah ya kara da cewa, daga watan maris zuwa yau dalibai 11 ne suka mutu a makarantar kuma an kasa gano wacce irin cuta ce.

Ya ce, ma'aikatan lafiya da hukumomin makarantar za su zauna su tattauna kan batun binciken gano wacce iri cuta ce.

A baya an taba gudanar da bincike kan ko cutar sankarau ce ke kashe daliban amma bayan bincike aka gano ba ita ba ce.

Tag: Mutuwa , Ajali , Gana , Cuta , Ciwo

Labarai masu alaka