Mahama ya hori matasan Afirka da su bar yin gudun hijira mai hatsari

Tsohon Shugaban Kasar Gana John Dramani Mahama ya shawarci matasan Afirka da su daina gudun hijira zuwa nahiyar Turai ta tekun Mediterrenean inda dubununnan mutane suka dilmiye.

A jawabin da ya yi ga taron Tarayyar Afirka karo na 6 kan Sulhu a Tsarin Demokradiyya da aka gudanar a Afirka ta Kudu, Mahama ya bayyana cewa, matasa su ne makomar Afirka a yanzu da kuma nan gaba.

Ya ce, matasa masu shekaru kasa da 35 ne kaso 65 cikin 100 na al'umar Afirka da suka haura biliyan 1.

Tsohon shugaban na Gana ya kara da cewa, babban abinda ke hana su bacci shi ne neman hanyoyin da za su ba wa matasa aiyukan yi.

Ya kuma ce, a kwanan nan ya saurari wata tattaunawa da wani matashi da aka dawo da shi Gana daga Turai wanda kafin tafiyarsa iyayensa suka tara masa dala dubu 6,500 don ya je Turai ya samu rayuwa mai kyau.

Mahama ya bayyana mamakinsa kan yadda wannan matashi ba zai iya amfani da wadannan kudade ba wajen juya wa tare da yin karamin kasuwanci.

Dubunanna 'yan Afirka ne ke bi ta kasar Libiya don zuwa nahi,yar Turai da nufin samun rayuwa ingantacciya amma da yawa daga cikinsu suna rasa rayukansu a teku.Labarai masu alaka