Sama da mutane dubu 1 cutar Kwalara ta kashe a Kongo

Mutane sama da dubu 1 ne suka mutu sakamakon kamu wa da cutar Kwalara a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo a wannan shekara.

Sama da mutane dubu 1 cutar Kwalara ta kashe a Kongo

Mutane sama da dubu 1 ne suka mutu sakamakon kamu wa da cutar Kwalara a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo a wannan shekara.

Ma'aikatar Lafiya ta kasar ta ce, a shekarar 2017 mutane dubu 47,370 ne suka kamu da cutar inda dubu 1,025 daga ciki suka rasa rayukansu.

Sanarwar ta ce, a tsakanin 20 da 26 ga watan Nuwamba mutane dubu 1,749 ne suka kamu da cutarinda 52 daga cikinsu suka mutu.

Ana hasashen cewa, sakamakon yadda babu kayan kula da lafiya yadda ya kamata ya sanya ba a iya magance cutar sosai.

Kungiyar Likitocin Komai da Ruwanka ta ce, rashin tsaftataccen ruwan sha ne ke janyo kamuwa da cutar a kasar.

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa, a shekarar da ta gabata mutane dubu 29,352 ne suka kamu da cutar inda 817 daga cikinsu suka rasa rayukansu.Labarai masu alaka