Sama da 'yan Najeriya 400 aka mayar gida daga Libiya

'Yan Najeriya 401 da ake tsare da su a kasar Libiya ne aka mayar gida a cikin kwana dayan da ya gabata.

Sama da 'yan Najeriya 400 aka mayar gida daga Libiya

'Yan Najeriya 401 da ake tsare da su a kasar Libiya ne aka mayar gida a cikin kwana dayan da ya gabata.

Wasu mutum 257 ne suka fara isa kasar tasu a ranar Laraba inda wasu 144 suka biye musu baya.

Kakakin Ofishin 'yan sandan filin tashi da saukar jiragen na Murtala Muhammad da ke Legas Joseph Alabi inda ya ce, mutanen sun hada da mata manya 65, maza manya 179yara kanana 7 da jarirai 6 wadanda 4 daga cikinsu ke bukatar taimakon gaggawa.

Mayar da 'yan najeriyar kasarsu ya biyo bayan suka da kasashen duniya ke yi kan ana sayar da bayi bakaken fata a Libiya.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce, har yanzu akwai akalla 'yan kasar 2,700 da suke a tsare a Libiya.Labarai masu alaka