"Kisan Gaddafi somin tabi ne"

Wani tsohon mashawarcin marigayi Mu'ammar Gaddafi, ya ce kisan tsohon shugaban kasar Libiya somin tabi ne na wani tsararren makircin da Amurka da kasashen Yamma suka shirya wa shugabannin kasashen Musulmai.

"Kisan Gaddafi somin tabi ne"

Wani tsohon mashawarcin marigayi Mu'ammar Gaddafi, ya ce kisan tsohon shugaban kasar Libiya somin tabi ne na wani tsararren makircin da Amurka da kasashen Yamma suka shirya wa shugabannin kasashen Musulmai.

Bashir Salah ya ce:

"Babu wani juyin juya halin da ya afku a Libiya,gambizar kasashen Yamma ne suka kulla wannan makarkashiyar don kashe Gaddafi da wasu shugabannin kasashen Musulmai,a ciki har da Masar da kuma Tunusiyya.Domin a ganin su Musulunci babbar barazana ce ga manufofin da suka gaba na mallakar duniya.Abinda yasa suka kuduri aniyar halaka duk wani shugaban da ya kalubalanci akidarsu.Kuma wannan somin tabi ne,saboda bukatar Amurka da kawayenta shi ne, su raba Islama da matsayinta na "Addini" don su maida ta "Zallar Al'ada" wacce ke kunshe da raye-raye,wake-wake da sauran shagulgulan raha.Abinda suke kira da  'Raba zaki da hakoransa, don ya zama tamkar magen gida'.Ta hakan ne kawai,zasu iya cin karansu babu babbaka.Amurka ta yi zaton cewa, Gaddafi na kyamar al'adun Yamma.Abinda yasa, a tsawon watanni 8 kasashe 40 suka fafata yaki da Libiya".

 


Tag: Gaddafi

Labarai masu alaka