Ana ci gaba da boren adawa da tsadar rayuwa a Tunisiya

Al'umar Tunisiya na ci gaba da adawa da matakan da gwamnatin kasar ta dauka na tsuke bakin aljihu wanda hakan ya jefa su cikin halin matsi da tsadar rayuwa.

Masu zanga-zangar sun taru a tsakiyar Tunus babban birnin kasar inda suka yi tattaki har zuwa bakin ginin ofishin gwamnan Tunus tare da tare hanyoyin mota da ma na tsayar da aiyukan jami'an taro.

Mutanen sun dinga daga allunan gargadar gwamnati tare da sukar matakan tsuke bakin aljihu da ta dauka wanda suka ce ya jefa su cikin halin matsin rayuwa.

Masu zanga-zangar sun din yin arangama da jami'an tsaro.

Al'umar sun saka wa zanga-zangar tasu sunan "Me kuke jira".

A watan da ya gabata ma al'umar Iran da Sudan sun gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasashensu.Labarai masu alaka