Magoya bayan Barrow da Jammeh sun fafata rikici a Gambiya

Rundunar 'yan sanda Gambiya ta hana duk wasu tarukan siyasa a kasar sakamakon rikicin da aka fafata a tsakanin magoya bayan tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh da masu goyon bayan gwamnatin hadaka karkashin Adama Barrow.

Rundunar 'yan sandan ta ce, dalilin da ya sanya aka dakatar da tarukan siyasar shi ne, rikicin da aka samu a Mankamang Kunda da ke yankin Upper River a gabar tekun yammacin gambiya.

Sanarwar ta biyo bayan kai jami'an tsaron Gambiya zuwa garin Busumbala mai nisan kilomita 31 daga Banjui babban birnin kasar don su kwantar da tarzoma.

Jami'an tsaron ECOMIG da ke kaar tun bayan fitar Jammeh ma sun je garin tare da shugaban rundunar sojin Gambiya Momodou Badgie.

An fara rikicin ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da magoya bayan Jammeh suka shiga yankin Kombo mafi girma a kasar bayan wani zagayen motsa jam'iyya da suka yi a fadin Gambiya.

'Yan jam'iyyar sun ce, wasu mutane ne suka dinga jifan motarsu da duwatsu wanda hakan ya sa su mayar da martani.Labarai masu alaka