Adadin wadanda zazzabin Lassa ya kashe a Najeriya ya kai mutum 37

Ya zuwa yanzu mutane 37 cutar zazzabin Lassa ta kashe a Najeriya da ke yammacin Afirka.

Adadin wadanda zazzabin Lassa ya kashe a Najeriya ya kai mutum 37

Ya zuwa yanzu mutane 37 cutar zazzabin Lassa ta kashe a Najeriya da ke yammacin Afirka.

Cutar dai ta bulla a jihohi 16 na kasar.

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya WHO ta fitar da alkaluman cewa, a makonni 5 a Najeriya mutane 450 cutar ta kama wadanda 37 daga ciki suka mutu.

A makon da ya gabata hukumomin ma'aikatar lafiya ta Najeriya sun ce, mutane 32 cutar ta kashe bayan bullar ta a jihohi 16.

Ana daukar cutar daga kashin bera inda mutum na iya harba wa dan uwansa mutum.Labarai masu alaka