Yadda birrai suka cinye Naira miliyan 70 a gidan gonar wani Sanata a Najeriya

A Najeriya dabbobi na ci gaba da lakume kudaden gwamnati inda bayan wani maciji da ya hadiye Naira miliyan 36 makwanni 2 da suka gabata, a yanzu ma wasu birrai sun yi awon gaba da Naira miliyan 70 mallakar Kungiyar Sanatocin Arewacin Kasar.

Dan Majalisar Dattawa daga jihar Kaduna Sanata Shehu Sani ya shaida wa Majalisar Dattawan dalilan da ya sa suka cire Sanata Abdullahi Adamu daga matsayin Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya.

Sanata Sani ya ce, sun dauki matakin ne sakamakon yadda Sanatan ya ce, wani biri a gonarsa ya cinye Naira miliyan 70 mallakar kungiyar tasu.

Sanatocin na Arewacin Najeriya sun zabi Sanata Aliyu Magatakarda Wammako a matsayin sabon shugabansu.

Makwanni 2 da suka gabata ma wata ma'aikaciyar Hukumar Shirya Jarabbawar Shiga Jami'a a Najeriya  JAMB ta ce, maciji ya hadiye Naira miliyan 36 a ofishinsu da ke jihar Benue.

Najeriya dai kasa ce da ta jima tana fama da matsalar cin hanci da rashawa wanda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi alkawarin yaka a lokacin da yake yakin neman zabe.Labarai masu alaka