Sanusi Jaku: Zabarmawa sun tsani Hausawa

Zazzafar sa-insa ta barke a Jamhuriyyar Nijar,inda a yanzu haka dubban mutane ke ci gaba da yin tofin Allah tsine ga mashawarcin shugaban kasar,Sanusi Jaku wanda ake tuhuma da neman hura wutar kabilanci.

A ranar 4 ga watan Fabrairun bana,Jaku wanda yayi ikirarin cewar, mambobin hadakan jam’iyyun siyasa na adawa (FOI) sun ci zarafinsa, tare da neman aika shi lahira babu gaira babu dalili.

Abinda yasa ya garzaya tashar rediyon Amfani,inda ya ce,Zabarmawa (Kabila ta 2 a Nijar a fannin yawa, 22 % ) na kyamar Hausawa ( Kabila mafi rinjaye a Nijar, 53 %).

Wannan furucin yayi matukar bakanta wa ‘yan Nijar, musamman ma Zabarmawa wadanda suka ce Jaku ya ci zarafin kabilarsu, haka zalika yana neman hura wutar kabilanci.

Abin  yayi matukar tada kura a shafukan intanet da kafofin yada labarai,har ta kai ga shugabannin Nijar suka yi tsokaci kan wannan tabun tare da yin alkawarin hukunta dukannin wadanda ke da hannun dumu-dumu a wannan lamarin.

Kafafan yada labarai na Jamhuriyar Nijar, sun tabbatar da cewa a ranar Litinin din nan ta gabata,’yan an tisa keyar Sanusi Jaku da shugaban tashar rediyo ta Amfani, Grema Bukar  zuwa helkwatar ‘yan sanda,inda daga bisani aka gurfanar su gaba kotu don jin ta bakinsu.

 Labarai masu alaka