UNICEF: Boko Haram ta yi garkuwa da yara kanana sama da dubu tun daga shekarar 3013

Asusun Tallafawa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2013 zuwa yau ‘yan ta’addar Boko Haram sun yi garkuwa da yara kanana sama da dubu daya a Najeriya.

A wata sanarwar da UNICEF ta fitar kafin gudanar da tarukan tuna wa da garkuwa da ‘yan matan Chibok shekaru 4 da suka gabata da ‘yan ta’addar suka yi, an bayyana cewa, ‘yan Boko Haram sun tsananta kai wa yara kanana hari tare da hana su karatun boko.

Sanarwar ta ce, ‘yan ta’addar Boko Haram sun raba miliyoyin yara kanana da matsugunansu.

Akalla akwai ‘yan matan Chibok 112 da suka rage a hannun Boko Haram, inda a ranar 19 ga watan Fabrairu ma suka sake garkuwa da wasu yaran mata 112 a makarantarsu da ke garin Dapchi na jihar Yobe a yankin arewa maso-gabashin Najeriya.

Wakilin UNICEF a Najeriya Mohamed Malick Fall ya bayyana cewa, taron tuna wa da garkuwa da ‘yan matan Chibok bayan shekaru 4 na nuna yadda ‘Yan ta’adda ke jefa rayuwar yara kanana cikin mawuyacin hali a yankin arewa maso-gabashin Najeriya.Labarai masu alaka