Mataimakin Shugaban Najeriya zai bayar da shaida kan batun zargin almundahana

Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo zai bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Kasar don bayar da shaida kan zargin almundahana da ake yi wa wasu jami’an gwamnati da aka dakatar a Hukumar Bayar da Agaji ta Kasa.

Majalisar Dokokin Najeriya na aikin gudanar da binciken zargin almundahanar kudade a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA.

Daga cikin wadanda ake bincike har da shugaban Hukumar Mustafa Maihaja.

Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Kan Magance Annoba Ali Isa ya shaida wa wani taron sauraren ra’ayin jama’a a Abuja cewa, Mataimakin Shugaban Najeriya zai bayyana a gaban kwamitin don bayar da shaida kan yadda aka dakatar da wasu jami’an Hukumar 6 saboda sun nuna ba su amince da yin almundahana ba.

Osinbajo ne shugaban Kwamitin Gudanarwar Hukumar wadda Majalisar ta ce, ita ce ta dakatar da mutanen 6.

Rahotanni sun ce, an dakatar da mutanen ne saboda sun nuna rashin amince wa wajen bayar da kwangilar miliyoyin daloli ba bisa ka’ida ba. Haka kuma ana zargin ana karkakatar da kayan taimakon da aka tanada don wadanda ta’addancin Boko Haram ya shafa.

Dan majalisar ya kara da cewa, shugaban Hukumar yaki da cin hanci da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya EFCC Ibrahim Magu da shugaban Hukumar Hana Fasa Kauri Hamid Ali za su bayyana a gaban kwamitin don bayar da shaida.

Ana yawan zargin Hukumar ta NEMA da aiyukan cin hanci da rashawa inda a shekarar da ta gabata ma aka samu Sakataren gwamnatin Najeria Babachir David Lawal da kashe Nairavmiliyan 200 wajen yanke ciyawa a sansanin ‘yan gudun hijira.Labarai masu alaka