'Yan sanda 5 sun mutu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a Najeriya

'Yan sanda 5 ne suka mutu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a Najeriya da ke Yammacin Afirka.

'Yan sanda 5 sun mutu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a Najeriya

'Yan sanda 5 ne suka mutu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a Najeriya da ke Yammacin Afirka.

Jami'in Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA a jihar Borno Bashir Garba ya bayyana cewa, 'yan ta'addar sun kai hari kan cibiyar 'yan sanda da ke garin Konduga inda suka kashe jami'ai 5 tare da jikkata wasu da dama.

Garba ya ce, an kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti inda ake kuma gudanar da bincike.

A shekarun 2000 aka kafa kungiyar ta'adda ta Boko Haram  amma kungiyar ta fara kai hare-hare a shekarar 2009 bayan kama wa tare da kashe shugabanta Muhammad Yusuf.

An kashe dubunnan mutane inda dubunnan daruruwa suka yi gudun hijira sakamakon rikicin na Boko Haram.Labarai masu alaka