Najeriya ta musanta halartar taron bude ofishin jakadancin Amurka a Kudus

Daya daga cikin Hadiman Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan kafafan yada labarai Bashir Ahmad ya fitar da sanarwa ta shafin Twitter inda ya ce, Kasar ba ta halarci taron bude sabon ofishin jakadancin Amurka a birnin Kudus ba.

Sanarwar ta biyo bayan suka da korafi da ‘yan Najeriya suka dinga yi kan cewa, jakadan Kasar a Isra’ila ya halarci bude ofishin.

Wasu kafafan yada labara da suka hada da Aljazeera sun bayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da suka halarci bikin amma daga baya sai suka cire ta.

A shekarar da ta gabata ma a Zauren Majalisar Dinkin Duniya Najeriya ta jefa kuri’ar kin amince wag a yunkurin Amurka na mayar da ofishin jakadancinta na Isra’ila da ke Tel Aviv zuwa Kudus.Labarai masu alaka