Nijar ta jaddada goyon bayanta ga Falasdinu

Jamhuriyyar Nijar ta jaddada goyon bayanta ga kasar Falasdinu da kuma alhinin Falasdinawa 62 da suka shi shahada a fagen gwagwarmayar hana Trump maida Qudus helkwatar kasar Yahudu.

A wani jawabin barka da gabatowar azumin watan Ramalana da yayi wa al'umarsa,firaministan Nijar Birgi Rafini ya ce,

"Tunani ya karkata kungurungu kan al'umar kasar Falasdinu,musamman ma na yankin zirin Gaza,wadanda a kwanakin ga suka fuskanta rashin imani marar misaltuwa.Gwamnatin kasarmu na jajanta wa Falasdinu tare da jaddada goyon bayanta ga 'yan uwanmu Falasdinawa.Muna Allah wadai da kisan gillar da Isra'ila take ci gaba da yi musu".

A ranar Litinin din nan da suka gabata ,sojojin Isra'ila sun kashe akalla Falasdinawa 62 tare da jikkata wasu 3188,yayin da suke yunkurin hana mayar da ofishin jakadancin Amurka birnin Qudus.

Wannan kisan kiyashin wanda ba shi ne farko ba, ya yi matukar bakantawa duniya ga baki daya, musamman ma Musulmai,wadanda kawo yanzu suek ci gaba da yin tofin Allah tsine kan Amurka, Isra'ila da kanzagansu.Labarai masu alaka