Tunisiya ta la'anci Isra'ila sakamakon zaluntar Falasdinawa da ta ke yi

Shugaban Kasar Tunisiya Al-Baji Ka'id Al-Sibsi ya yi suka tare da la'antar munanan aiyukan da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa.

Tunisiya ta la'anci Isra'ila sakamakon zaluntar Falasdinawa da ta ke yi

Shugaban Kasar Tunisiya Al-Baji Ka'id Al-Sibsi ya yi suka tare da la'antar munanan aiyukan da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa.

Sanarwar da Fadar Shugaban Kasar ta fitar ta ce, a tattaunawar da Sibsi ya yi da Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas inda suka tattauna mummunan halin da Falasdinawa suke ciki a lokacin da ake zanga-zangar ranar Nakba da ta afku shekaru 70 da suka wuce.

Sanarwar ta kuma ce, Tunisiya na yabon Falasdinawa da ke zanga-zangar lumanar neman 'yanci, kare tsarkakakkun wurare da tsare kasarsu.

Haka zalika Tunisiya ta yi fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka inda ta kuma mika sakon ta'aziyyar mutanen da suka yi Shahada.Labarai masu alaka