Kifewar kwale-kwale ya yi sanadiyrar rasa rayuka 7 a Sokoto

Kifewar kwale-kwale mai ɗauke da mutane 30 a Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya saboda tsananin iska ya yi sanadiyyar rayuka 7.

Kifewar kwale-kwale ya yi sanadiyrar rasa rayuka 7 a Sokoto

Kifewar kwale-kwale mai ɗauke da mutane 30 a Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya saboda tsananin iska ya yi sanadiyyar rayuka 7.

Kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa a Sokoto lbrahim Dingyadi ya bayyana cewar tsananin iska ya sanya kifewar kwalekwale mai ɗauke da mutane 30 a rafin Bafarawa dake jihar Sokoto a Najeriya. 

Dingyadi, ya ƙara da cewa bayan hatsarin an ceto mutane 8 a inda kuma aka gano gawawwaki 7 inda kuma ake ci gaba da neman sauran mutane 15.

Wadanda aka ceto an garzaya dasu asibiti inda kuma ake ci gaba da gudanar da aiyukan ceto sauran kamar yadda Dingyadi ya bayyana.Labarai masu alaka