Fatuma Ahmed,sabuwar Manjo Janar ta Kenya

A Kenya, wata Musulma ta zama mace ta farko wacce aka taba nadawa a matsayin Manjo Janar ta sojojin kasar.

Fatuma Ahmed,sabuwar Manjo Janar ta Kenya

A Kenya, wata Musulma ta zama mace ta farko wacce aka taba nadawa a matsayin Manjo Janar ta sojojin kasar.

Wannan shi ne karo na farko da wata Musulma da ta taba rike irin wannan babban mukamin.

Yayin wani bikin rantsarwa da aka gudanar a Nairobi, babban birnin kasar, shugaba Uhuru Kenyata ya ce ya nada Fatuma a matsayin manjo janar ta sojojin kasarsa, sabon ta zama gagara misali ga sauran matan Kenya,inda ya ce:

"...Halartar bikin rantsar da manjo janar mace ta farko a tarihin kasarmu, babban abin alfahari ne da farin ciki".Da fatan za ki zama abin kwatance ga sauran matan wannan jamhuriyyar.Za ki nuna musu cewa, babu wani kalubale a gabansu"

Kenyatta ya kuma yi wa sojojin kasarsa alkwararin kawar da barazanar ta'addanci daga Kenya.
 Labarai masu alaka