Rundunar Sojin Najeriya ta musanta an yi garkuwa da sojojinta kusan 600 a Bama

Rundunar Sojin Najeriya ta fitar da sanarwa inda ta musanta labaran da ake yada wa na an yi garkuwa da sojojinta kusan 600.

Kakakin Rundunar Sojin Najeriya Birgediya Janar Texas Chukwu ya bayyana cewa, a karshen makon da ya gabata an samu arangama tsakanin 'yan ta'addar Boko Haram da sojoji a yankin Bama na jihar Borno.

Chukwu ya ce, karya ne labaran da ake cewa na sojoji sun yi rikici da 'yan Boko Haram kuma an yi garkuwa da sojoji 600 da tankokin yaki 8, kawai dai sojoji 2 sun jikkata sakamakon lamarin.

Chukwu ya kuma kara da cewa, an kashe 'yan ta'adda 22 tare da jikkata wasu da dama a yayin rikicin da suka fafata da sojoji.

Amma wata majiya ta ce, a garin Gaidam na jihar Yobe ne aka yi garkuwa da sojojin ba wai a jihar garin Baman jihar Borno ba.Labarai masu alaka