An kama 'yan ta'addar Boko Haram 22 a Najeriya

A yayin wasu farmakai da aka kai a Najeriya an kama 'yan ta'addar Boko Haram 22.

An kama 'yan ta'addar Boko Haram 22 a Najeriya

A yayin wasu farmakai da aka kai a Najeriya an kama 'yan ta'addar Boko Haram 22.

Kwamishinan 'yan sanda Damian Chukwu da ya fitar da sanarwa a madadin rundunar 'yan sandan Najeriya ya ce, an kai farmakai kan 'yan ta'addar Boko Haram a yankunan Bama da gwoza da ke jihar Borno.

Chukwu ya ce, a yayin farmakan an kama 'yan ta'adda 22 kuma 8 daga cikinsu na daga cikin wadanda suka yi garkuwa da 'yan matan Chibok tare da shirya kai wasu munanan hare-hare na kunar bakin wake sama da 50 a jihohin Adamawa da Borno Labarai masu alaka