Dandal Kura,sabon numfashin Borno

Wasu matasa a jihar Borno, sun yanke shawarar yin tsayin daka da nufin hana jama'a rungumar mummunar akidar Boko Haram,wacce ke ci gaba da halaka dubban Musulmai a Najeriya,Nijar,Kamaru da Chadi, ba gaira ba dalili.

Dandal Kura,sabon numfashin Borno

Wasu matasa a jihar Borno, sun yanke shawarar yin tsayin daka da nufin hana jama'a rungumar mummunar akidar Boko Haram,wacce ke ci gaba da halaka dubban Musulmai a Najeriya,Nijar,Kamaru da Chadi, ba gaira ba dalili.

Makamin da wadannan matasan wadanda dukanninsu ke yin aiki tukuru a gidan rediyon Dandal Kura International, shi ne hada karfi da karfe da malamai wajen waye wa jama'a kai,musamman ma matasa wadanda zaman kashe wando da kuma kucin rayuwa ke ci gaba da karkata akalar rayuwarsu a sauwake, zuwa alkiblar Boko Haram.

A yanzu,Dandal Kura wacce ke yada shirye-shiryenta tsawon awanni shida a kowace rana, na zaman kanta,maimakon a da,inda kasashen Amurka da Burtaniya ne ke daukar nauyinta.

Tuni tashar ta samu karbuwa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya da ma wasu kasashe makwabta,wadanda suka hada da Nijar,Kamaru da Chadi.

Manufar, rediyon wanda ya kaura daga jihar Kano zuwa Maiduguri a watan Fabrairun shekarar 2016,ita ce yada ingantattun akidojin Islama don samar da dauwamammen zaman lafiya da kuma waye wa al'uma kai kan gurbatacciyar fassarar ayoyin Al Kur'ani mai tsarki da 'yan Boko Haram ke yi wajen cusa wasiwasi a zukatan matasa da kuma wadanda iliminsu na addini bai taka kara ya karya ba.

 Labarai masu alaka