• Bidiyo

A legas malama Kirista ta hadu da fushin Musulmai

A  binin Legas na Tarayyar Najeriya wata malamar sakandari Kirista ta hadu da fushin al'umar Musulman yankin, sakamakon yadda ta ci zarafin wasu dalibai mata 5 tare yi musu korar kare,sabili sun zo makaranta sanye da hijabi.

A legas malama Kirista ta hadu da fushin Musulmai

A  binin Legas na Tarayyar Najeriya wata malamar sakandari Kirista ta hadu da fushin al'umar Musulman yankin, sakamakon yadda ta ci zarafin wasu dalibai mata 5 tare yi musu korar kare,sabili sun zo makaranta sanye da hijabi.

Lamarin dai ya afku ne a ranar Larabar nan da ta gabata a makarantar sakandari ta Isolo da ke Legas, inda wata malama Kirista mai suna J.O Shadare ta tirsasa dalibanta cire hijabinsu da kuma tisa keyarsu zuwa gidajensu,inda ta ce suturarsu haramtacciya duba da dokokin makarantar.

Wannan abun bakin cikin ya fusata Muslman Legas matuka gaya, inda tuni suka fara yin tofin Allah tsine kan malamar, ganin yadda take neman haramta abinda tuni dokokin yankin suka hallata.

Duba da dokokin Legas, kowace mace na 'yancin rufe kanta ko kuma a'a.

A ranar Asabar din nan da ta gabata,mataimakin gwamnan Legas,kana kwamishinan ilimi, Idiat Adebule ya yi tsokaci kamar haka:

"Tuni muka dage Misis Shadare zuwa wani yankin, don gudun kar abin ya haifar da tashe-tashen hankula tsakanin mabiya addinai daban-daban da ke Legas.Zamu kuma, zurfafa bincike kan lamarin.A ranar Litinin mai zuwa,zamu gudanar da wani taro da zummar shawo kan wannan abun.Muna fatan mutane zasu sanyaya zukatansu kafin nan.Saboda wannan matsala ce da ta shafi hukuma.Kuma babu makawa, zasu magance ta.Kamata ya yi al'uma ta san da cewa, doka daya ce,sandar hukunci kuma,a hannun shugabanni take.Don haka, kar fushi ya makanta su har ta kai su ga daukar hukunci da karan kansu".
 Labarai masu alaka