Rundunar sojan Najeriya ta kashe ƴan ta'addar Boko Haram 76
An bayyana cewar fafatawar da aka yi tsakanin yan ta'addar Boko Haram da rundunar sojojin Najeriya sojoji 7 sun rasa rayukansu a yayinda aka kashe 76 daga cikin ƴan ta'addar.

An bayyana cewar fafatawar da aka yi tsakanin yan ta'addar Boko Haram da rundunar sojojin Najeriya sojoji 7 sun rasa rayukansu a yayinda aka kashe 76 daga cikin ƴan ta'addar.
Rundunar sojan Najeriya ta bayyana cewar a wani fafatawar da tayi da ƴan ta'addar Boko Haram a Metele dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar ta tasa ƙyeyar ƴan ta'addar Boko Haram 76 barzahu.
Daga cikin sojojin 7 sun rasa rayukansu inda 16 kuma suka raunana.
A Chadi wacce ke makwabtaka da Najeriya an kashe ƴan ta'adda 48 inda sojoji 8 suka rasa rayukansu a wata fafatawar.
Ƙungiyar Boko Haram da ta ɓullo a shekarar 2000 ta yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane dubu 20 bayan ta fara kai hare-haren ta'addanci a shekarar 2009.
Kungiyar ta fara kai hare-hare a shekarar 2015 a ƙasashen dake makwabtaka da Najeriya da suka haɗa da Kamaru, Chadi da Nijer.
A hare-haren da ta kai a tabkin Chadi ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu biyu.