Boko Haram na ci gaba da sanya yin gudun hijira a Najeriya

A sakamakon hare-haren ta'addanci da ƙungiyar Boko Haram ke kaiwa a yankin Arewa maso gabashin Najeriya dubun dubatan mutane sun yi ƙaura daga gidajensu.

Kodinetan hukumar bayar da tallafi ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya Erdward Kallon ya bayyana cewar  a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sakamakon ƙaruwar hare haren ta'addanci fiye da mutane dubu 30 sun tilastu da barin gidajensu.Kallon da ya ƙara da cewa kungiyar Boko Haram ta kwace sansanin soja biyu ya tabbatar da:

"Sanadiyar ƙaruwar kai hare-haren ta'addanci a yankin Maiduguri fiye da mutane dubu 30 sun yi ƙaura zuwa sansanin ƴan gudun hijira"

Kallon ya bayyana cewar wadanda ke zuwa mafakar ƴan gudun hijirar na bukatar abinci, ruwan sha da sauran kayyayaki.

Kungiyar Boko Haram da ta ɓulla a shekarar 2000 sanadiyar hare-haren ta'addanci na ƙin ƙari da ta fara ƙaddamar wa a shekarar 2009 kimanin mutane dubu 20 sun rasa rayukansu.

Daga shekarar 2015 kawo yanzu hare haren kungiyar a ƙasashen Kamaru, Chadi, Nijer da yankin tabkin Chadi kimanin mutane dubu biyu sun rasa rayukansu.Labarai masu alaka