Tshisekedi ya lashe zaben Shugaban Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo an sanar da sunan Felix Tshisekedi a matsayin wnda yalashe zaben Shugaban Kasar da aka gudanar a ranar 30 ga watan Disamba.

Tshisekedi ya lashe zaben Shugaban Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

A Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo an sanar da sunan Felix Tshisekedi a matsayin wnda yalashe zaben Shugaban Kasar da aka gudanar a ranar 30 ga watan Disamba.

Sanarwar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta fitar ta ce, kaso 57.56 na masu jefa kuri’a ne suka yi zaben.

Sanarwar ta ce, dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta UDPS Tshisekedi ya samu kaso 38.57 na kuri’un da aka kada, sai dan takarar hadin gwiwa na wasu jam’iyyun adawa da suka hada kai Martin Fayulu ya samu kaso 35.2 inda dan takarar hadaka na gwamnati Emmanuel Ramazani Shadary ya samu kaso 23.8.

Akwai bukatar kotun tsarin mulki ta amince da sakamakon nan da ranar 15 ga watan Janairu.

A gefe guda kuma, mahaifin Felix Tshisekedi mai suna Etinne Tshisekedi ne ya fafata a zaben watan Nuwamban shekarar 2011 tare da shugaba mai ci Joseph Kabila.

‘Yan adawa sun bayyana cewar a zaben da aka sanar da Kabila a matsayin wanda ya yi nasara Tshisekedi ne ya samu rinjaye.

Bayan mahaifinsa ya rasu a shekarar 2017 ne sai Felix Tshisekedi mai shekaru 55 ya zama shugaban jam’iyyarsu.

A ranar 11 ga watan Nuwamban bara Tshisekedi ya sanar da goyon baya ga dan takarar hadin gwiwa Martin Fayulu amma sakamakon martanin ‘yan jam’iyyarsa ya sanya shi janye wananna goyon baya kwana guda bayan furta shi.

A shekarar 2016 aka shirya gudanar da zabe a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo amma sakamakon matsalolin tsaro da kudi ya sanya aka dage lokacin.

Shugaban kasar Mai ci Jpseph Kabila da ya shugabanci kasar tun 2001 ya kammala wa’adinsa da kundin tsarin mulki ya ba shi.

Hukumar zabe ta shirya gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Disamba amma sakamakon kamawar gobara a ofishinta tare da konewar kaso 80 na kayan zabe a Kinsasha ya sanya aka dage zuwa ranar 30 ga Disamban.

Sakamakon yaduwar cutar Ebola a yankunan Beni da Butembo an dage lokacin zabe har sai watan Maris.Labarai masu alaka