BH na ci gaba da salwanta rayuka a Najeriya

Wata Arangama da ta barke tsakanin rundunar sojojin Najeriya da 'yan haramtacciyar kungiyar Boko Haram a garin Baga na jihar Borno ya rutsa da rayukan mutane 2 , inda wasu 5 kuma suka jikkata.

BH na ci gaba da salwanta rayuka a Najeriya

Wata Arangama da ta barke tsakanin rundunar sojojin Najeriya da 'yan haramtacciyar kungiyar Boko Haram a garin Baga na jihar Borno ya rutsa da rayukan mutane 2 , inda wasu 5 kuma suka jikkata.

Kakakin rundunar sojin kasar Najeriya,Birgedia Janar Sani Kukasheka Usman ya ce, sojojin sun mutu yayin wani samame da suka kai a yankin Baga wanda ya kasance a karkashin ikon Boko Haram.

Usman ya ce, sun yi nasarar kwace iko da garin na Baga,amma sojoji 2 sun rasa rayukansu,inda wasu 5 kuma suka jikkata sakamakon wata arangama da ta barke tsanakin su da 'yan ta'adda.

Boko Haram wacce ta fara kunno kai a Najeriya tun a wajejen shekarar 2000, ta kashe sama da mutane dubu 20,000 tun a lokacin da ta fara kai hare-haren ta'addanci a shekarar 2009 ya zuwa yau.

Tun daga shekarar 2015 kawo yanzu, kungiyar ta tsalake iyakokin Tarayyar Najeriya,inda take ci gaba da zubda jinin wadanda basu ji ba su gani ba a kasashe makwabta,wanda suka hada da Kamaru,Chadi da kuma Jamhuriyyar Nijar tare da salwanta akalla rayukan mutane dubu 2,000 a yankin Tafkin Chadi.

Gabatar da tsohon kakakin Boko Haram,Abu Musab Al Barnawi da aka yi a shekarar 2016 a matsayin sabon shugaba,ta haifar da mummunar baraka da kuma tashe-tashen hankula marasa misaltuwa tsakanin sa da Abubakar Shekau wanda ke jan akalar wannan haramtacciyar kungiyar tun daga shekarar 2009 ya zuwa yau.
 Labarai masu alaka