Sandar shari'a ta doke babban alkalin Najeriya

A karo na farko a tarihin kasar Najeriya aka taba hukunta wani babban alkali sakamakon zargin sa da ake da ta fafka karya game da ainahin arzikin da ya mallaka.

Sandar shari'a ta doke babban alkalin Najeriya

A karo na farko a tarihin kasar Najeriya aka taba hukunta wani babban alkali sakamakon zargin sa da ake da ta fafka karya game da ainahin arzikin da ya mallaka.

A ranar Asabar din nan ne aka sanar da cewa an wannan karo sandar shari'a ta doke babban alkalin Tarayyar Najeriya sabili da ya yi zuki tamalle kan bayanan da ya bada game da takaimamen dukiyar da ya tanada.

Wannan sanarwar dai ta fito ne daga Ofishin Ladaftar da ma'aikata ta CCB ta Hukumar yaki da cin hanci da rashawa,inda aka tabbatar da za a gurfanar da Walter Onnoghen gaban kotun CCB ranar Litinin nan mai zuwa sakamakon tuhumar sa da ake yi da aikata wasu manyan laifuka shida.

Wata jaridar kasar Najeriya mai suna Daily Trust ta raiwato cewa, gwamantin Najeriya na zargin babban alkali Walter da yin bayanin karya game da ainahin arzikin da ya mallaka da kuma tanadar wani asasun banki wanda ke cike makil da kudaden kasashen ketare a muhallinsa.
A duk tarihin Najeriya ba a taba gurfanar da wani alkali gaban kotu ba yayin da ya kai kan aikinsa sai a wannan karon. A shekarar 2015, Hukumar CCB ta tuhumi shugaban majlisar sanatoci ta kasar da aikata laifin almundahanai,amma babbar koyun kasar ta watsar da wannan zargin.Labarai masu alaka