An kashe sojojin Yaman 6 a wani harin bam
Sojoji 6 ne suka mutu sakamakon harin bam da wata mota da aka kai a garin Aden na kasar Yaman.

Sojoji 6 ne suka mutu sakamakon harin bam da wata mota da aka kai a garin Aden na kasar Yaman.
Bayanan da aka samu daga majiyoyin yankin na cewa, an kuma jikkata wasu mutane 14 a harin wanda aka nufi cibiyar 'yan sandan yankin Shaihk Usman da ke garin Aden wanda nan ne helkwatar wucin gadi ta gwamnatin Yaman.
An sanar da cewa, ginin cibiyar ya rushe yadda ba zai moru ba,kuma wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin halin rai mutu kwakwai.