Wani toron Giwa ya kashe 'yan yawon bude ido a Zambiya

'Yan sandan kasar Zambiya sun bayyana cewa, wani toron giwa ya kashe 'yan yawon bude ido a garin Livingstone da ke kasar wanda ke jan hankalin 'yan kasashen waje.

Mukaddashin shugaban 'yan sandan yankin Danny Mwale ya fada wa 'yan jarida cewa, mutanen da giwar ta kashe sun hada da 'yar kasar Beljiyom maishekaru 55 da da najimi mai shekaru 64 daga kasar Holan.

Mwale ya ce, 'yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru inda suka ga gawarwakin mutanen 2 a kusa da kogin Lodge.

An kai jikkunan mutanen zuwa asibitin Batoka kuma ba a bayyana sunayensu ba. Ana ci gaba da bincike kafin a yanke shawarar binne su a kasar ko kma mayar da su kasashensu.

Mwale ya kara da cewa, 'yan sanda kuma na ci gaba da bincike ko dai mutanen sun kashe kansu da kansu ne.

Hukumar Kula da Namun Dajita Zambiya ta sanar da cewa, dabbobin dawa na kashe daruruwan mutane a kasar musamman ma 'yan yawon bude ido daga kasashen waje.Labarai masu alaka