Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.12.2017

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.12.2017

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya  07.12.2017

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.12.2017

Babban labarin Sabah na cewa shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya kira taron gaggawa na ƙasashen Musulmi da za'a gudanar a ranar 13 ga watan Disamba akan yunkurin shugaban ƙasar Amurka Donal Trump na maida birnin Qudus babban birnin lsra'ila.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa jamiyyun huɗu na Majalisar Dokokin Turkiyya sun ƙalubalanci yunƙurin Trump na mai birnin Qudus amatsayin babban birnin lsra'ila da babban murya. 

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa Al'ummar Turkiyya ta ƙalubalanci yunkurin Trump na mai birnin Qudus amatsayin babban birnin lsra'ila. Da yawan al'umma ƙasar sun cika titunan manyan biranen ƙasar domin nuna rashin amincewarsu akan yunkurin shugaba Trump.

Babban jaridar Hürriyet na cewa kamfanin jiragen Turkiyya Turkish airlines dana Rasha Aeroflot sunyi wata yarjejeniya da zasu fara gudanar da sufuri kai tsaye daga birnin Antaliyan Turkiyya zuwa birnin Moscow Rasha sau bakwai a rana.

Babban labarin jaridar Haber Türk na cewa taliyar garin Konya da aka fara yi 1998 ya samu bunƙasa tare da haɗin gwiwa hukumar kimiyya da fasaha ƙasar. Taliyar dake dauke da bitamin da maadanan gina jiki da dama za'a fara fitar dashi zuwa ƙasashe goma da suka haɗa da Japan

 

 Labarai masu alaka