'Yan yawon bude ido dubu 13 sun shiga halin tsaka mai wuya a Swizalan

Sakamakon zubar dusar kankara kamar da bakin kwarya a wajen wasannn zamiya na Zermatt da ke Swizalan 'yan yawon bude ido sun shiga halin taska mai wuya.

Sakamakon kwanaki 2 da kankarar ta dauka tana zuba an rufe hanyoyin mota da na jirgin kasa.

An bayyana cewa, a yankunan da suke da iyaka da Italiya ne aka fi samun munanar lamarin.

An kwashe wasu mutane 100 da jirage masu saukar ungulu daga yankin Zermatt.

Ana ci gaba da kokarin share hanyoyin yankin.Labarai masu alaka