Gidan Sinima na farko a Saudiyya ya fara nuna fina-finai

Bayan shekaru 35 a karon farko gidan Sinima ya fara nuna fina-finai a Riyadh Babban Birnin Saudiyya.

Gidan Sinima na farko a Saudiyya ya fara nuna fina-finai

Bayan shekaru 35 a karon farko gidan Sinima ya fara nuna fina-finai a Riyadh Babban Birnin Saudiyya.

Kamfanin Kula da Walwalar Jama'a da ke Cibiyar Sarki Salman tare da Asusun Zuba Jari na Saudiyya ne suka hada gwiwa da daya daga cikin manyan kamfanunnukkan duniya mai suna "American Multi-Cinema" (AMC) tare da kafa gidan Sinimar.

Ministan Raya Al'adu da Sadarwa na Saudiyya Awad bin Salih Al-Awad, Mataimakiyar Darakta Janar kan Harkokin Wasanni kuma Shugabar Hukumar Harkokin Wasanni ta Kasar Gimbiya Rima bint Bender tare da Shugaban Mataimakin Shugaban AMC Jason Cole da sauran manyan baki ne suka halarci bikin bude gidan Sinimar.

Sanarwar da Ma'aikatar Raya Al'adu da Sadarwa ta Saudiyya ta fitar ta ce, bayan shekaru da dama a karon farko an bude g,idan Sinima a Riyadh Babban Birnin Kasar amma za a fara gwaj,na mako guda sannan sai a ci gaba da sayarwa da jama'a tikiti ta yanar gizo.

An bayyana cewa, an tsara gidan Sinimar ta yadda jama'a za su ji dadin kallo sosai.

Da fari za a fara sayar da tikitin shiga kan dala 13 wato Riyal 50 amma daga baya kudin zai ragu.Labarai masu alaka