Turkiyya ta gina katabaren Masallaci a Jamus

Kungiyar Haddin Kan Musulmi ta Ma'iakatar Addinin Turkiyya (DİTİB) ta bude wani katabaren masallaci a garin Aachen dake kasar Jamus.

Turkiyya ta gina katabaren Masallaci a Jamus

Kungiyar Haddin Kan Musulmi ta Ma'iakatar Addinin Turkiyya (DİTİB) ta bude wani katabaren masallaci a garin Aachen dake kasar Jamus.

Taron bude masallacin da hukumar Yunus Emre ta jagoranta ya samu halartar shugaban kungiyar yankin Armin Laschet da kuma gwamnan arewacin Ren Vesfalya .

Jakadan Turkiyya a garin Koln Baris Ceyhun Erciyes ya bayyana cewar bude masallacin na nuni da irin zaman lumana da akeyi a yankin tsakanin addinai.

Inda shi kuma Armin Laschet ya bayyana cewar al'umar yankin zasu ci gaba da mutunta juna da zama cikin lumana. Inda ya yi kira da kar a maida wuraren ibada tamkar fagen siyasa, inda ya kara da cewa kasancewar Hukumar Yunus Emre a kasar abin alfaharine sosai.

Mataimakin ministan harkokin addinin kasar Turkiyya Osman Tiraşçı ya yi kira ga musulman yankin da su yi amfani da masallacin wajen koyar da kyakyawar tabi'ar addinin Islama su kuma kauce wa dukkan lamurkan dake bata wa addinin suna.

 Labarai masu alaka