An hana Kiran Sallah a Kudus saboda bikin sauya wa ofishin jakadancin Amurka gari

Gwamnatin Kasar Falasdin ta bayyana cewa, amfani da uzurin taruka wajen hana kiran Sallah a Birnin Kudus take hakkin Addini ne ga Musulmai.

Ministan Al'amuran Addini Kungiyoyi Yusuf Edis ya bayyana cewa, su ba su amince da matakin hana kiran Sallah da gwamnatin Birnin kudus ta yi ba.

Edis ya ce, daukar wannan mataki ya zama kokarin rufe bakunan Musulman da ke Kudus.

Ministan ya kara da cewa, wannan mataki da aka dauka a ranar da Amurka ke mayar da ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa Kudus ba abun amince wa ba ne kuma ba zai haifar da da mai ido ba.

Gwamnatin Kudus ta sanar da cewa, sakamakon bukukuwan murnar mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Kudus daga Tel Aviv ya sanya sun hana kiran Sallah a ranar Litinin din nan a Kudus.Labarai masu alaka