Youtube zai fara yaki da labaran karya a shafinsa

Shafin yada bidiyo na Youtube sanar da fara yaki da labaran karya da ake saka wa ta shafin nasa.

Youtube zai fara yaki da labaran karya a shafinsa

Shafin yada bidiyo na Youtube sanar da fara yaki da labaran karya da ake saka wa ta shafin nasa.

Sanarwar da mamallakin Youtube da ke da mallakin Google ta ce, a wani bangare na yaki da labaran karya za su samar da tsarin da masu amfani da shafin za su samu labarai na gaskiya kuma masu inganci.

Sanarwar ta ce, daga yanzu duk labaran da masu amfani za su saka Youtube zai gansu kuma za su tabbatar da gaskiyar labaran da aka saka kafin su isa ga jama'a.

A gefe guda Youtube ya yi alkawarin zuba jarin dala miliyan 25 don samar da labarai ingantattu.Labarai masu alaka