An gano sassan wani dan maciji mai shekaru miliyan 99

A Kasar Myammar da ke nahiyar Asiya an gano sassan wani dan maciji da ya ke da shekaru miliyan 99.

An gano sassan wani dan maciji mai shekaru miliyan 99

A Kasar Myammar da ke nahiyar Asiya an gano sassan wani dan maciji da ya ke da shekaru miliyan 99.

Tashar yada labarai ta Ingila BBC ta bayar da labarin cewa ba kasafai aka cika samun irin wannan burbushe na halitta ba kuma sakamakon yadda bishiya ta lullube shi ya sanya ya samu kariya.

Farfesa Michael Caldwell na jami'ar Alberta da ke Kanada ya bayyana cewa, sassan dan macijin mai shekaru 99 da aka samu shi ne mafi tsufa a duniya da aka taba gani ya zuwa yanzu kuma ya rayu a dazukan Myammar a zamanin Kretase.

An bayyana cewa, burbushen itatuwa da kwarin da aka gani a kan sassan jikin macijin ne ya ke tabbatar da a ina kuma a wanne zamani ya rayu.Labarai masu alaka