'Yan yawon bude ido na bayyana gamsuwarsu ga wuraren shakatawa na Turkiyya

A wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da Kungiyar 'Yan Kasuwar Trabzon (TTSO) inda aka gano cewar masu zuwa yawon bude ido daga yankunan Gulf na zama a Turkiyya har tasawon kwanaki 7.6. Kuma kowanne mutum idan ya zo yana kashe akalla dala dubu 2,340.

Ma'aikatan (TTSO) ne suka gudanar da kuri'ar ta jin ra'ayin 'yan yawon bude ido a filin tashi da saukar jiragen sama na Trabzon a watan Satumba.

Sakamakon da aka nuna ya bayyana kaso 81.5 na 'yan yawon bude idon ya gamsu matuka inda kaso 16,9 kawai ya gamsu inda kaso 1.6 ba su gamsu yadda ya kamata ba.

Babu wani dan yawon bude ido da ya bayyana bai ji dadin shakatawa a yankin na Trabzon ba.Labarai masu alaka