Za a haramta saka Nikabi a Italiya

Hukumomin gudumar Trino da ke garin Vercelli na kasar Italiya sun kammala shirye-shiryen haramta wa mata Musulmai saka Nikabi a yankunansu.

Za a haramta saka Nikabi a Italiya

Hukumomin gudumar Trino da ke garin Vercelli na kasar Italiya sun kammala shirye-shiryen haramta wa mata Musulmai saka Nikabi a yankunansu.

Kamfanin dillancin labarai na ANSA da ke Italiya ya ce, a wannan makon haramcin saka Burka zai fara aiki a gundumar ta Trino.

Mataimakin Shugaban gundumar Trino dan jam'iyyar LP mai kyamar 'yan gudun hijira Roberto Rosso ya bayyana cewar duk matar da aka kama ta saka Nikabi za a ci tarar ta Yuro 500.

Rosso ya ce, Nikabi wani tufafi ne da ba a saba gani a yankin ba kuma dokar tasu na nufar wasu mata ne su 3.

Wasu 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar LP a makon da ya gabata sun bukaci a hana saka Nikabi a yankin Bergamo mai nisan kilomita dari da hamsin daga Trino.Labarai masu alaka