“Duk a lokacin da na ceci rayuwa nakan ji tamkar na shiga Aljannah”

An karrama wani dan kasar Turkiyya mazauni Ostraliya sabili da ceton rayuwar wani yaro dan shekaru 17.

“Duk a lokacin da na ceci rayuwa nakan ji tamkar na shiga Aljannah”

An karrama wani dan kasar Turkiyya mazauni Ostraliya sabili da ceton rayuwar wani yaro dan shekaru 17.
Candan Baykan, 52, mai gadi a babbar kasuwar Melbourne ya samu karramawa inda aka bashi lambar yabo mai taken St. John’s Ambulance Save a Life Award a Sydney.

Baykan ya yiwa yaron tausar kirji bayan yaron ya fadi inda ya suma nan take saboda rashin lafiya ta alaji.,
Baykan, wanda ya kwashe shekaru 23 yana zaune a Ostraliya ya bayyana cewar yayi farin ciki kwaran gaske ganin yadda yaron ya farfado. Ya kara da cewa nakan kasance cikin farin ciki tamkar na shiga aljanna duk a lokacin da na ko naga an ceci rayuwa.

Karramawa da aka yiwa Baykan karramawace da ake baiwa wadanda suka yi wani abin azo gani ko wani kwarjini a cikin shekara.

 Labarai masu alaka