An yi jana'izar tsohon Shugaban Kasar Amurka Bush

An yi jana'izar tsohon Shugaban Kasar Amurka George H. W. Bush a birnin Washington wanda ya mutu yana da shekaru 94 a duniya.

An yi jana'izar tsohon Shugaban Kasar Amurka Bush

An yi jana'izar tsohon Shugaban Kasar Amurka George H. W. Bush a birnin Washington wanda ya mutu yana da shekaru 94 a duniya.

A ranar 30 ga watan Nuwamba Bush ya mutu a jihar texas inda aka kai Washington Babban Birnin Amurka don yi masa jana'iza.

A shekaran jiya ne aka yi taron girmmawa ga Bush a Majalisar Dokokin Amurka inda da safiyar Larabar nan kuma aka yi jana'izarsa.

Jerin gwanon motocin dake dauke da Bush sun wuce ta gaban Fadar White House inda aka tafi da shi zuwa Babbar Cocin Amurka ta Cathedral.

Shugaban Kasar Amurka Donald Tump tsaffin shugabannin kasar Jimmy Carter, Bill Clinton da Barack Obama ma sun halarci taron.

Jikokin Bush, tsohon Firaministan Kanada Brian Mulroney da masanin tarihi John Meacham na daga cikin wadanda suka yi bayani.

Dan gidan Bush kuma tsohon Shugaban Kasar Amurka George W. Bush ne ya karanta bayan yabo ga baban nasa.Labarai masu alaka