An buɗe ofishin hukumar Yunus Emre a Koriya ta Kudu

An bude ofishin hukumar Yunus Emre (YEE) a Seul babban birnin ƙasar Koriya ta Kudu.

An buɗe ofishin hukumar Yunus Emre a Koriya ta Kudu

An bude ofishin hukumar Yunus Emre (YEE) a Seul babban birnin ƙasar Koriya ta Kudu.

Hukumar wacce ɗaya daga cikin hukumomin ci gaban ƙasar Turkiyya ce ta buɗe ofishin ta tare da haddin gwiwar jami'ar Hankuk dake karantar da yaruka dadan daban a ƙasar ta Koriya ta Kudu.

Ɗaya daga cikin maaikatan hukumar YEE dake Seul Özgür Can Yıldız da jakadan Turkiyya a Seul Ersin Erçin sun ziyarci gurin inda sunka yi tofa albarkacin bakinsu akan ayyukan hukumar.

A kalaman jakada Erçin a fagen taron ya nuna farin cikinsa akan yadda hukumar zata fara gudanar da ayyuka irin na al'adun Turkiyya a ƙasar ta Koriya ta Kudu. A kalaman sa ya bayyana cewar hukumar zata gudanar da ayyuka a ƙasar da sunka amince da al'adun Turkiyya da kuma al'umar ƙasar. Ayyukan zasu kasance ta fannoni biyu: Na farko dai shi ne koyar da sanarda yaren Turkanci, bunƙasa zaman takewa tsakanin ƙasashen biyu da kuma bunƙasa fannin buɗe ido.Na biyu kuma za'a ɗauki matakan rage karfin lamurkan kungiyar ta'addar FETO a ƙasar.

 

Yıldız kuwa ya bayyana cewar hukumar YEE da zata fara gudanar da ayyuka a watan Fabrairu a Koriya ta Kudu na gudanar da ayyuka fiye da dubu da 200 a cikin shekara a fadin duniya.

Yıldız ya ƙara da cewa babban manufarsu shi ne karfafa hurɗa da wadanda ke hurɗa da Turkiyya da kuma kara yawan su a ƙasar.

 Labarai masu alaka