Harin bam a gidan gwamnatin Afganistan

Mutane 11 sun rasu a wani hari da a ka yi a bangaren bâƙi wanda ke gidan gwamnatin garin Kandahar na kasar Afganistan.

Harin bam a gidan gwamnatin Afganistan

Mutane 11 sun rasu a wani hari da a ka yi a bangaren bâƙi wanda ke gidan gwamnatin garin Kandahar na kasar Afganistan.

Harin ya yi sababin jin ciyon gomnan Kandahar, Humayun Azizi da kuma jakadan Dubai na garin Kabil, Muhammad Abdullah el-Kabi sannan da wasu mutane guda 15.

Shugan tsaron na garin Kandahar, Abdul Razzak ya ce an yi harin ne yayinda gomna Aziz da jakadan Dubai, El-Kabi da sauran wakilai na musamman suke ganawa a bangaren bâƙi na gidan gwamnatin garin.

Razzak ya kara da cewa ana tsammanin an maƙala bamabaman ne a karkashen kujerun gidan baƙin sannan a ka tada bamabaman daga nesa.

Razzak ya bayyana cewa harin ya janyo rasuwar mutane 11, a cikin wadanda suka rasun kuwa a kwai wakilai na masamman. Sannan ya kara da cewa gidan baƙin ya kone sakamakon harin.

Haka zalika yace an kasa gano ainahin mutanen 11 da suka rasu sabida konewar gawawwakinsu. Sai kuma ya kara da cewa mutane 15 ne suka ji rauni wadanda cikinsu akwai gomna Azizi da ku ma jakadan Dubai, El-Kabi.

An ce gomnan da mataimakinsa na cikin jinya mai tsanani sakamokon harin.

Yanzu dai babu wani labarai game da yanayin lafiyar sauran baƙin ‘yan diflomassiyyan.

A babban birnin kasar, Kabul kuwa; mutane 30 ne suka mutu yayinda 70 sukaji ciyo sakamakon wasu hare-hare biyu da aka yi a kusada ginin majisar kasar.

Kungiyar Taliban ta bayyana cewa ita ce tayi harin.

A lokaci guda, kasar Turkiyya ta bayyana matukar fushinta ga harin yayinda ta yi ta’aziyya ga kasar Afganistandin da mutanen kasar wanda ta kira ‘yan uwanta.

Ma’aikatan harkokin kasar wajan Turkiyya tayi bayani kamar haka:

“Muna da tabbas kan cewa irin wadannan hare haren ba zai sa kasar Afganistan ta durkusawa ‘yan ta’adda ba. Turkiyya za ta taimakawa mutanen Afganistan din da ta take ganin su a matsayin ‘yan uwa. Taimako irin wanda za su iya bukata dan magance ta’addanci da taimako a sauran bangarorin rayuwa.”

 

 

 

 Labarai masu alaka