• Bidiyo

Kotun Ƙolin Amurka tayi watsi da buƙatar Trump akan hana Musulmi zuwa Amurka

Babban kotun Amurka ta yi watsi da buƙatar shugaba Trump na dakatar da Musulmi daga ƙasashe shidda daga shiga Amurkan.

Kotun Ƙolin Amurka tayi watsi da buƙatar Trump akan hana Musulmi zuwa Amurka

Babban kotun Amurka ta yi watsi da buƙatar shugaba Trump na dakatar da Musulmi daga ƙasashe shidda daga shiga Amurkan.

Kamar yadda kotun ta bayyana a rubuce, yunkurin hana Musulmi zuwa Amurka da Trump ya ɗauka a ranar 24 ga watan Satumba ya saɓawa dokar kasar.

Haka kuma ɗaukar wata mataki da zai rage zuwan Musulmi a ƙasar ma bai dace ba.

A baya dai shugaba Trump ya dauki matakin hana Musulmin ƙasashen lran, lraqi, Siriya, Somalia, Libiya da Sudan zuwa Amurka, lamarin da Musulmi ƙasashen suka nuna rashin amincewarsu.

 Labarai masu alaka