Pentagon: Daesh ce ta kai wa sojojinmu hari a Nijar

Ma'aikatar Tsaro ta Amurka Pentagon ta bayyana cewa, sun tabbatar da 'yan ta'addar Daesh ne suka kai musu harin kwantan bauna a kudu maso-gabashin Nijar a lokacin da suke aiki tare da sojojin kasar.

Kakakin Sashen Kula da Afirka a Pentagon Manjo Michelle Baldanza ta ce, a ranar 4 ga watan Oktoba ne aka kashe sojojin Amurka 4 a wani hari da 'yan ta'addar Daesh suka kai.

Ta ce, Tabbas 'yan ta'addar Daesh ne suka kai harin amma kuma domin samun cikakken bayani suna ci gaba da gudanar da bincike.

Wani jami'in tsaron Amurka da ya tattauna da kafafen yada labaran kasar amma ba a bayyana sunansa ba ya ce, 'yan ta'adda 15 ne suka kai harin.

A makon da ya gaba ne Ofishin Tsaron na Amurka mai kula da Afirka ya bayyana cewa, an kashe sojojinsu 3 da na Nijar 4 a wani hari da aka kai musu a lokacin da suka kan hanyar dawowa daga wani taro da suka gudanar da shugabannin kabilu a iyakar Nijar da Mali.

Daga baya kuma aka sake ganon gawar wani sojan na Amurka da ya bace.Labarai masu alaka