Koriya ta Arewa ta sake jan kunnen Amurka game da yiwuwar fara luguden Nukiliya

Wakilin Koriya ta Arewa a Majalisar Dinkin Duniya Ja Song Nam ya yi gargadin cewa, Amurka da Koriya ta Kudu da suke gudanar da atisayen hadin gwiwa na kara ingiza yiwuwar fara yakin Nukiliya.

A wata wasika da Ja ya aike wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, atisayen da Amurka ta gudanar da jiragen yaki 'yan kwanakin nan na kara rura wutar rikcin tsibirin Koriya, kuma sakamakon haka ana cikin mummunan hali a yankunan.

Ja ya kara da cewa, a lokacin da ake yakin cacar baki amma sai ga shi Amurka kuma na yin atisaye da jiragen yaki da ka iya harba makamin Nukiliya samfurin B-52.

Ya ce, sakamakon haka kasarsa na gardar Amurka da hawainiyarta ta kiyayi ramar Koriya ta Arewa.

An bayyana cewa, atisayen da Amurka da Koriya ta Kudu ke yi da jiragen ruwa na yaki 3 samfurin USS Nimitz, USS Theodore Roosevelt, USS Ronald Reagan da kuma jiragen sama 11 zai ci gaba har zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.Labarai masu alaka