Mutane sama da 400 ne suka mutu sakamakon girgizar kasa a iyakar Iran da Iraki

Rahotanni da aka samu na cewa, mutane sama da 400 ne suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a kan iyakar kasashen Iran da Iraki wadda ke da karfin awo 7.3.

Mataimakin Daraktan Hukumar Magance Annoba ta Iran Behnam Saidi ya tattauna da kafar talabijin din kasar inda ya ce, mutane 407 ne suka mutu inda wasu dubu 6,700 suka samu raunuka a Iran kadai.

Daraktan hukumar Isma'il Najjar kuma ya ce, sakamakon yadda girgizar ta afku a waje mai girma ya sanya ana shan wahala wajen aiyukan ceto.

Ya ce, Kauyukan Kasri Shirin da Serpulzihab ne suka fi lahanta sakamakon girgizar. Yanki mai girma ya rushe, a saboda haka aikin ceto na fuskantar matsaloli da dama.

Dubunnan 'yan kasar Iran da gidajensu suka rushe sun kwana a tantunan da aka samar musu.

 Labarai masu alaka