'Yan ta'addar Taliban sun kashe 'yan sanda 22 a Afganistan

A garin Kandahar na kasar Afganistan 'yan sanda 22 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Taliban suka kai musu.

'Yan ta'addar Taliban sun kashe 'yan sanda 22 a Afganistan

A garin Kandahar na kasar Afganistan 'yan sanda 22 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Taliban suka kai musu.

Kakakin Rundunar 'yan Sandan Kandahar Ziya Durani ya bayyana cewa, a yammacin Litinin din nan ne 'yan ta'addar suka kai hari a ofishin 'yan sanda na gundumomin Mayvend da Jirey inda suka jikkata karin 'yan sanda 15.

Durani ya ce, harin ya dauki tsawon awanni 2, kuma an kashe 'yan ta'addar Taliban 40 tare da jikkata wasu 35 a fafatawar da aka yi.

Kungiyar Taliban kuma ta ce, ta kashe sama da jami'an tsaro 40 a harin.Labarai masu alaka