An kashe fitulun Masallacin Aksa mai girma

Bayan matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka kan Masallacin Aksa mai girma wanda ka iya janyo rikici a birnin Kudus da Yahudawa suka mamaye, an kashe fitulun Masallacin baki daya.

An kuma ga cewa, an kashe fitulun wurin shakatawa na Cocin Mehd da aka haifi Annabi Isah Alaihissalam kamar yadda mabiya Addinin Kirista ke fada.

A ranar 5 ga watan Yunin shekarar 1967 ne Isra'ila ta mamayi Kudus kuma a shekarar 1980 ta sanar da cewa, nan ne Helkwatarta.

A shekarar ta 1980 Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, wannan mataki da Isra'ila ta dauka haramtacce ne kuma ba ta amince da shi ba.

A hukuncin na Kwamitin an amince Yahudawa sun mamayi Gabashin Kudus. Dukkan ofisoshin jakadancin kasashen duniya na birnin Tel Aviv. Babu wata kasa da ta amince da Kudus a matsayin Helkwatar Isra'ila.Labarai masu alaka